Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Na Shirin Rage Yawan 'Yan Wasa Da Kulob Zai Bada Aro


Hukuma kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA na shirin rage yawan 'yan wasa da kulob zai bayar a matsayin aro a kowace kakar wasa don kare kungiyoyi masu tasowa.

Hukumar kula da kwallon kafa ta ba da shawarar bayar da ‘yan wasa shida kacal a matsayin aro daga kulob a kowacce kakar wasa.

FIFA ta bayyana wa wakilai daga kungiyoyin kwallon kafa da hukumomin shirya lig lig na Duniya, gami da na 'yan wasa' Fifpro da membobin kungiyar tarayya a wani taro da sukayi a ranar Litinin.

Amma har yanzu dole ne sai an cimma yarjejeniya tare da wasu masu ruwa da tsaki a wasanni, ciki har da kulob, kulob da 'yan wasan - game da abin da ya kamata ayi kan wannan lamarin.

Sabon tsarin zai iya shafar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, wanda ake kiyasin tana da 'yan wasa 40 da ta tura aro a wannan kakar wasa. Haka kuma FIFA za ta sake gabatar da tsari na jami'an ‘yan wasa wato wakilai a bangaren saye da sayarwa a lokacin rani na shekarar 2019.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG