Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiddausi Sani: Karancin Jari Bai Hana Fara Sana'a


Fiddausi Sani
Fiddausi Sani

Na fara sana’ar hannu ne ta hanyar amfani da kafofin sadarwa na zamani, wajen tallata hajata tare da samun kwastomomi masu sayen kayan, a cewar matashiya Fiddausi Sani.

Fiddausi dai ta fi amfani da shafukan sadarwa na zamani kamar su WhatsApp, ko Instagram inda da zarar mutum na bukata sai ya tuntubeta a shafukan ta na yanar gizo, daga nan sai a aika kudi ta account dinta, sa'annan ita kuma sai ta aika wa mai bukata ta mota a tasha, idan ba a gari daya mabukacin yake ba.

Ta dai fara sana’ar sayar da kayan mata kamar su leshe da atamfofi ne bayan ta je sayen kayanta na amfanin kanta a kasuwa, sai suka bata sha’awa sai ta dauki hotonsu ta sa a kan shafin whatsapp, kafin wani lokaci mutane sun fara tambayar nawa suke, kamar wasa sai ta saro kayan naira dubu dari a cewarta shi kenan, silar fara sayar da kaya a gida ta hanyar amfani da kafar zamani kenan.

Fiddausi, ta kara da cewar, a duk lokacin da mutane ke bukata kayan da suka gani da gaggawa, ta kan kai kayan tashar jirgin sama ta aika kayan ta jirgin sama, amma duk wanda ya sayi kayan shi zai bada kudin kaiwa wanda ake cewa Courier services a turance.

Ta fara sana’ar ne ganin yadda ta ga sana’ar hannu ke taimakawa mata wajen dauke masu kananan bukuta a cewar matashiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG