Hauwa’u Abdullahi, ta ce ta fara sana’ar hannu ne domin ta zama mai dogaro da kai da kuma sauke wa iyayenta dawainiya, a cewarta ta fara sana’ar kitso ne ba tare da ta koya daga wajen kowa ba.
Hauwa’u ta ce idan aka tura ta gidan kitso tana lura da yadda mai kitson take saraffa gashi, da haka da haka idan ta dawo gida sai ta rika koya akan mahaifiyarta.
Matashiya Hauwa’u ta bayyana cewa tana kisto ne kafin ta samu gurbin karatu a makarantar gaba da sakandare, ta ce a yanzu tana zaman jiran takardar shiga jami’a ne kuma ko da ta samu gurbin karatun zata cigaba da sana’arta ta hannu.
Ta ce ko da ta kammala karatunta na sakandare bata tambaye iyayenta kudin bikin kammala karatu, wato graduation ba, da kudin kitson da take samu ta tara ta kuma biya wa kanta wannan kudi.
Haka kuma ta ja hankalin ‘yan uwanta matasa da su zamo masu kwazo da jajircewa wajen cika burukansa mussaman ma wadanda suka danganci ayyukan hannu
Ta kara da cewa tana samun kasuwa ne a lokutan bukukuwan sallah da Kirsimeti, sannan tana da burin bude shagon kitso da zata rika wannan sana’a kafin ta samu kwas din da take sha’awa na Physiotherapy.
Facebook Forum