Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Zanga-zangar Adawa Da Dokar Mallakar Bindiga A Amurka


Kyrgyzstan - Kyrgyz police, security, force, army, spetsnaz, militia, crime, gun, generic, undated
Kyrgyzstan - Kyrgyz police, security, force, army, spetsnaz, militia, crime, gun, generic, undated

Masu goyon bayan kowa ya mallaki bindiga a Amurka sun gudanar da zanga-zanga a jihohi daban-daban

Wasu masu goyon bayan mallakar bindiga anan Amurka sun gudanar da zanga-zangar lumana a jiya asabar.

Masu zanga-zangar wadanda suka yi maci zuwa majilisar dokokina jihohin Amurka daban-daban suna sukan lamirin masu kira ne da a samar da doka mai tsaurin gaske da zaisa a rage samun damar mallakar bindiga, suna cewa wannan ya take musu hakkin sun a mallakan makamai.

Musali Masu zanga-zangar sunyi gangami daga Dalaware to Wyomin, kuma mutane daban-daban ne cikin su suka yi jawabi.

Abinda ko suke cewa shine gargadi akan samar da doka mai tsanani akan mallakar bindiga wanda daga bisani ma ana iya hana mallakar bindigar dungurungun.

Daya daga cikin masu jawabin a wurin gangamin Westley Williams yace idan kanada gini kuma kullun kana cire bulo daya daga cikin ginin ai wata rana ka wayi gari ka taras ba ginin.

Wastley wanda ke dauke da bindiga a wurin zanga-zangar kamar sauran wasu da suke dauke da ita suna yaci gaba da yiwa juna jawabi a harabar babban kotun kolin Wyoming.

Masu zanga-zangar dai sun shirya shi ne a dukkan jihohin dake Amurka kwanaki kadan bayan anyi wani babban gangami a nan Washington, New York da dai wasu manyan birane inda aka nuna bukatar ganin gwamnati tayi wani abu game da mallakar bindiga anan barkatai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG