A cewar Dawlat Waziri, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar, yan kunar bakin wake guda biyar ne suka kai harin. Biyu daga cikinsu sun tada nakiyoyinsu ne a daidai kofar shiga makarantar, sauran ukun kuma sukai kokarin shiga amma rundunar sojojin Afghanistan sun harbe biyu tare da kama guda.
Tuni kungiyar IS ta bayyana cewa ita ke da alhakin kai wannan harin ta kafar watsa labaran ta ta Amaq.
Wannan harin yazo ne a lokacin da kasar ke juyayin wani harin da aka kai a karshen satin da ya gabata wanda yai sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100 ciki har da ‘yan sanda da dama.
Daukacin kasar duk tayi zaman makoki a jiya Lahadi yayinda kuma shugaban kasar Ashraf Ghani ya bayyana yau Litinin ma ta zama ranar hutu saboda a samu damar taimakawa wadanda harin ya ritsa dasu.
Facebook Forum