Wasu majiyoyi a Najeriya sun ce hukumomi sun gano wasu hanyoyin da kungiyar Boko Haram, bangaren Abubakar Shekau, take bi wajen cusa wa yara kanana maza da mata akidar kai hare-haren kunar bakin wake, da kuma yadda suke bi wajen kaiwa.
Majiyoyin sun ce sashen kai hare-haren kunar bakin waken kungiyar Boko Haram bangaren Shekau shine ake kira "Majmu'at Tafjir" ko Sashen Fashe-Fashe a Hausa, kuma yana karkashin jagorancin Musa Abuja, mai alhakin juya kwakwalwar wadanda zasu kai harin, da karbo umurnin kai hari kai tsaye daga Abubakar Shekau.
Daya jigon wannan bangare na Majmu'at Tafjir kuwa shine Abu Darda, wanda hukumomin Najeriya suka kama shi a can baya, amma kuma suka sake shi domin musanyarsa da 'yan matan Chibok da aka sako kwanakin baya.
Wadannan bayanai su na daga cikin bayanan da suka bullo a tambayoyin da ake yi ma daruruwan 'yan Boko Haram da aka kama, ko kuma suka mika kawunansu a yayin da sojojin Najeriya suke ci gaba da kai musu raraka.
A saurari cikakken bayani na irin yadda Musa Abuja da Abu Darda suke kitsa kai hare-haren bam, da kuma irin shawarwarin matakan da 'yan Najeriya zasu iya dauka domin kare kawunansu.
Facebook Forum