Shugaban kungiyar kwallon kafar Super Eagle Mr. Gernot Rohr, ya yi Allah wadai da yadda aka zabi kasar Ingila, a matsayin kasar da za’a fafata wasan kasashen Afrika.
Ya kara da cewar hakan bai dace ba ko kadan, inda ya ce akwai bukatar wasa na gaba a maida shi wani wuri.
Kocin na magana ne, biyo bayan hana wasu ‘yan wasan kasar Burkina Faso, takardun shiga kasar Ingilar, wato 'visa', wanda hakan ya sa ba’a buga wasan ba.
‘Yan wasan na Najeriya sun buga wasa tsakanin su da ‘yan wasan kasar Senegal a ranar 23, ga wannan watan a matakin wasan sada zumunci.
Duk dai da cewar wasan bai zoma kocin yadda yaso ba, ganin ya na da matasa da yake son wasa su, sai ga wasan an tashi da ci 1-1.
Hakan dai ya sa ‘yan wasan Najeriya, cikin rukuni na uku a gasar cin kofin kasashen Afrika na 2017.
Mr. Rohr, ya ce ai duk suna da masaniyar yadda visa shiga kasar Ingila ke da wahala inda ya ce kamata ya yi a tsara wasan a filin wasa na Schengen, maima kon zuwa kasar Ingila.
Kocin ya kara da wasu daga cikin ‘yan wasan Najeriya ma ba su samu zuwa ba, sanadiyar samun visa a kurarren lokaci.
Rohr ya kuma ce yanzu suna duk wasu shirye shirye don tunkarar wasansu mai zuwa, wanda suke kokarin bama duk ‘yan wasan su damar buga wa, saboda da yawan su ba su buga wasa ba tun bayan barin su kungiyoyin su.