Shirye-shirye na gabda kammala na yunkurin gwamnatin kasar Portugal, don kokarin canza suna tashar jiragen sama na kasa-da-kasa mai suna ‘Madera International Airport’ zuwa sunan shahararren dan kwallon duniya ‘Cristiano Ronaldo’ duk dai da cewar akwai ‘yan adawa da basu yadda da sauya suna tashar ba, zuwa suna dan kwallon ba.
Ana sa ran dan wasan Ronaldo zai halarci bukin kaddamar da sabon sunan tashar, yanzu haka dai har an makala sababbin alamu, da hoton dan wasan a ko’ina na tashar. Canjin sunan tashar jiragen saman ya karbu tare da biye duniya.
Wanda ya jawo hankalin mutane da dama a kasar, da yawa daga cikin ‘yan siyasa suna adawa da wannan salon, na saka sunan dan kwallo a tsahar jiragen sama, hasalima suna ganin kamata yayi a saka sunan dan wasan a filin kwallon kafa ko wani gini dake da alaka da wasannin.
Wasu na sukar matakin gwamnatin yankin, don canza suna batare da tuntubar gwamnatin tarayyar kasar ba. Ganin da wasu keyi, cewar hakan bai yi dai-dai ba, shi kuwa shugaban kasar yankin Madeira, yana gani hakan abu ne da ya dace, ganin yadda Ronaldo, yayi suna a duniya, wannan wani abun fahariya ne ga kasar shi, kuma karrama shi wani abu ne da yayi dai-dai.