Kalubalen da masana’antar Kannywood ke fuskatanta bai wuce na rashin ilimin gudanar da fina-finan da suka dace da al’adar malam bahaushe ba, inji Mataimakin Shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa, Tjjjani Shehu Yahya.
Mataimakin shugaban kungiyar furodusoshi ta kasa Tijjani Shehu ne ya bayyanawa wakiliyar DandalinVOA a wata tattaunawa da ta yi dashi a jihar Kano.
Malamin ya kara da cewa ayyukan kungiyar sun hada da bada shawarwrin yadda masu shirya fina-finai zasu samu kasuwar hajjarsu tare da ba ‘ya‘yan kungiyar horon yadda zasu gudanar da harkokinsu.
Ya kara da cewa babu wani da zai fitar da fim ba tare da ya danganta kansa da wata kungiya ba ko kuma kungiyarsu ta karkashin kungiyar masu hada fina-finai ta kasa.
A kokarin inganta harkar fim ne ya sa gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da an bude wani kwas a jami’a da zai bada horo a kan harkar fim duba da rashin ilimin da wasu da ke cikin harkar gudanar da fim, kama daga shirya fina-finan da ma yadda za’a sayar da su a kasuwani.