Fin din kaabil, da akai alkawarin cewa zai fito a ranar 25, ga wannan watan da muke ciki, ya fito da kafar dama a Bollywood, inda masu kallo suka yaba da gagarumin aikin da wadanda suka shirya fim din suka yi.
Yawancin gidajen sinima din da aka nuna wanna sabon fim din sun cika makil babu masaka tsinke, kuma jama’a da dama da suka kalli fim din sun yaba dashi.
Wani daga cikin masu kallo yace rawar da Roshan ya taka a cikin fin babu kama hannun yaro domin sai da hawaye suka zubo mashi, ya kara da cewa wasu dattawa miji da mata da suka zauna kusa dashi a gidan kallo suma sun kasa daurewa sai da suka koka hawaye sharbe sharbe.
Daga matasa zuwa dattawa da suka kalli wannan fim din sun jinjina suna masu cewa lallai fim din ya cancanci yabo.
A yanzu haka dai fim din ya Samu karbuwa na kimanin kashi araba’in da biyar zuwa hamsin a cikin dari a rana ta farko 45-50, kuma ana sa ran cewa alkaluman zasu fi haka a nan gaba.
Fim din dai na wasu makafi ne wadanda daga bisani suka tsunduma cikin kogin soyayya tamkar tantabaru.
Tabbas, Roshan yana sane cewa bai taba yin fim din da ya fi wannan ba duk tsawon rayuwarsa a fagen fina finai.
Roshan shi kansa yace abin ya zo mashi da mamaki domin bai tsammaci cewa fim din zai taka irin wannan rawar ba , yana mai cewa ya samu labarin cewa jama’a, na ta shagulgulan murnar wannan fim din a cewarsa “ina mai godiya ga reku masoyana” kuma nayi alkawarin cewa zan kara kaimi wajan fina finai na domin ta haka ne kwai zan kara nuna godiya gareku.