Abba Almustapha, wanda aka fi sani da Abba ruda, ya shafe tsawon lokaci baya fitowa a finafinai, ya ce harkar fim harka ce da ke daukar lokaci da dama wanda hakan ya sa ya dakata domin karo ilimi tare da gudanar da kasuwanci da waiwayar rayuwa.
A yanzu dai jarumin ya dawo, ya kuma bayyana wa wakiliyar DandalinVOA wasu daga cikin dalilan da ya sa ya dakatar da harkar fim.
Ya ce ya shiga harkar fim a matsayin sana’a kamar kowa sannan a matsayinsa na matashi da ya lura abubuwan da ya ke nema a harkar fim ya samu sai ya ga cewar ya kamata ya koma domin karo ilimin boko da na ma kasuwanci don inganta harkar sa.
Ko da yake kafin ya dakatar da harkar fim, ganin irin daukakar da ya samu ya sa ya ga ya zama wajibi ya ingantata, ya fara fim da zummar inganta harshen Hausa da al’adunsu da ma iliminatarwa ta fina-finai.
Abba Ruda, ya ce wani hanzari ba gudu ba, suna fuskantar matsaloli musamman daga wajen masu kallonsu, ta inda suke wa masu sana’ar wata mummunar fahimta.
A tsegumin kuwa munan nan dauke da tsegumi daga jarumi Abba Ruda.