Majalisar Dokokin Najeriya na kokarin yin doka da zata rage yawan shekarun masu iya tsayawa takara saboda matasa su samu damar taka rawa a harkokin gudanar da Najeriya.
Dokar a yanzu haka ta samu karatu na biyu a majalisar dokokin Najeriya, dokar na neman a rage shekarun mai tsayawa takarar shugaban kasa daga shekaru arba’in, zuwa talatin, na kujeran Gwamna kuma daga shekaru talatin da biyar zuwa talatin, na ‘yan majalisar tarayya dana jihohi a rage daga shekaru dalati zuwa ashirin da biyar.
Wani dan majalisar wakilai Abdullahi Umar Faruk, yace gaskiya ya dace ayi wannan ragin shekarun domin a samu sa matasa a cikin milkin gudanar da kasa.
Bashir Muhammad Baba, mai nazarin al’amuran yau da kullum, na ganin yin haka wani abu ne mai kyau domin zai kawo zaman lafiya a kasa.
Itama shugaban kungiyar kare mata ‘yan ziyasa “Youth Teenage Politicians” Mercy Onyekwelu, tace in dai za’a yi irin wannan doka kuma ta dore a wanna kasa toh inna tare dasu dari bisa dari.
Ta kara da cewa kasashen dake baiwa matasa dama a fannoni daban daban na rayuwa zaki ga suna ci gaba sosai, kamar kasar China tana amfani da kwazon matasanta masamman ta kimiya da fasaha yasa sun ci gaba.