Dandalin sada zumunci na Twitter ya fitar da wasu hanyoyi da zasu taimaka wajen dakile cin zarafin mutane da kuma saukaka hanyar da za a iya sanar da rahotan cin zarafin.
Kafanin Twitter ya sanar da cewa ya kara fadada madangwalin kange hirar jama’a da mutum baya son ganin duk wani abu da suka rubuta ko suka kafe, yanzu haka mutane zasu iya rubuta wasu kalmomin da basu da ra’ayin ganin an tallata musu domin dakile su.
Sai dai kuma duk kalmomin da aka dakile zasu kasance kan dandalin Twitter ga duk wadanda basu kange ba su gani. Haka kuma kamfanin zai saukaka hanyar da mutane zasu iya mika rahotan duk wani rubutu na cin zarafi, hade da horas da ma’aikata kan kudurin kamfanin da ire iren yadda dabi’un cin zarafi suke.
Kamfanin Twitter dai ya dade yana kokarin samun mafita bayan da ya zamanto dandalin da mutane ke yada cin zarafi, yayin da yake kokarin kare matsayarsa kan barin mutane su fadin albarkacin bakinsu.