kungiyar malaman jami'oi ta Najeriya asuu ta fara wani yajin aikin gargadi na kwanaki 7 domin tunatar da gwamnati cika alkawarin data sanyawa hannu da kungiyar.
Ita dai kungiyar ta malaman jami’a na bukatar gwamnatin Najeriya ta biya ta wasu makudan kudade ne domin inganta harkokin ilimi a kasar kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bukaci a yi.
Yayinda wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Bababngida Jubrin ya zaga cikin jami’ar jihar Legas, daya daga cikin jami’o’in da malamanta suka shiga yajin aiki, koda shike bai sami zantawa da shugabannin makaratar ba, amma dalibai da dama sun mika kokensu ga gwamnati domin shawo kan lamarin.
Yanzu dai abin jira a gani shine ko gwamnatin tarayyar Najeriya zata biya dukkan bukatun kungiyar ta ASSU domin magance sake afkuwar tsunduma cikin yajin aiki nan gaba.
Ga rahoton Babangida Jubrin daga Legas.