WASHINGTON, DC —
An danganta nasarar dimokradiya, a Amurka, akan bin doka da oda, Aliyu Dabo Muhammad, wani dan Najeriya, mazaunin kasar Amurka ne ya bayana haka a hirarsu da wakilin mu Usman Kabara, akan zaben shugabancin Amurka da aka kammala.
Yace duk da yake jama’a, sun fi raja’a kan sakatariya Hillary Clinton, abinda sakamakon zabe ya kasance a bisa doka ya zama wajibi ya zama abin dogaro.
Ya kara da cewa bin doka da oda shike kawo ci gaba da kwanciyar hankali a kasa, kuma duk inda akwai bin doka akwai ci gaba.
Yana mai cewa ya kyautu kasashen Afirka, su koyi darasin bin doka domin nahiyar ta samu ci gaban da ya dace ta ita.
Dabo Muhammad, ya jinjinawa Najeriya, akan yadda ta tafiyar da zabenta da fatan hakan zai dore a zabubbuka nag aba masu zuwa.