WASHINGTON, DC —
Gwamnatin jihar Borno, na daf da fara koyar da dalibai a jami’ar, malakar jihar.
Darakata mai kula da hulda da jama’a da watsa labarai na hukumar kula da jami’oin Najeriya, Ibrahim Usman Yakasai, ne ya furta haka a wata hira da muryar Amurka.
Akan batun cinkoso a jami’oin Najeriya, kuwa daraktan cewa yayi suna da tsarin da ya baiwa kowace jami’a adadin daliban da zata dauka kowace shekara a bisa la’akari da yawan dakunan daukan darasi, dakuna kwaje kwaje da dakunan kwana .
Yakara da cewa cinkoson da ake samu a jami’oi, ba laifin hukumar dake kula jami’oi, bane domin a cewarsa wasu jami’oi, na karya dokokin da aka gindayamasu wanda ke da nasaba da daukan dalibai.