Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cristiano Ronaldo Da Gareth Bale Na Iya Samun Lambar Ballon d'o


An zabi shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo, da kuma Gareth Bale a matsayin wadanda suka can canci lambar yabo ta Ballon d’Or, wato fataccen dan wasan kwallon kafa na duniya, ‘yan wasan biyu na karkashin inuwa guda , wato suna takawa kungiyar kwanlon kafa ta Real Madrid leda.

A cikin jerin sunaye biyar na farko na ‘yan wasan Tamaula 30 da aka fitar da suka can canci shiga jerin sunayen wadanda za su lashe wannan lambar yabo sun hada da Sergio Aguero, da Pierre Emerick Aubameyang, da mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Italiya Gianluigi Buffon.

An bayyana daukacin sunayen ‘yan wasan da aka rabuta a rukuni biyar biyar na wadanda zasu lashe wannan kyauta a ranar litini.

A sheakarar 2010, an bada kyautar Ballon d’Or ta fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na shekarar data gabata na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ne a lokaci guda, amma a wannan shekarar, an sauya yanayin bada kyaututtukan zuwa yadda aka saba tun da farko, wato za’a bada kowace kyauta akan gashin kanta.

Sunan dan wasan cikin gida na kungiyar kwallon kafa ta Belgium Kevin De Bruyene da na dan wasan Manchester city, da kuma Atrhletico Madrid Antoine Griezmann na cikin jerin manyan sunayen da aka fitar daga baya bayannan.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG