Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatarorin Harkokin Wajen Amurka da Rasha Zasu Gana A Switzerland Ranar Asabar


Lavrov na Rasha da Kerry na Amurka
Lavrov na Rasha da Kerry na Amurka

Bayan da suka bijirewa juna makon jiya saboda abun da Amurka ta kira halin rashin son sulhuntawa da Rasha ta nuna yanzu kasashen biyu zasu sake ganawa a kasar Switzerland

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai hadu da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da wasu manyan abokai, a kasar Switzerland a ranar Asabar a wani yunkurin neman nemar hanyar diplomasiya ta warware rikicin Syria.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace tattaunawar ta birnin Lausanne tana cikin hanyoyin hadin guiwan kasashe biyo bayan daina tattaunawa kai tsaye da Rasha a kan tsagaita wuta da kuma kai kayar agajai a Syria.

Kerry zai kuma tattauna a kan batun Syria da wasu kawaye na yankin Larabawa da na kasa da kasa a ranar Lahadi a birnin London.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG