Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Na'urar "Juno" Ta Aiko Da Hoton Duniyar "Jupiter"


Duniyar Jupita
Duniyar Jupita

Hukumar binciken sararrin samaniya NASA, sun bayyanar da wani hoto a karon farko, da yake nuna gabashin duniyar Jupiter. Hoton yana nuna yanayin yadda iska da sauran hallitu ke rayuwa a duniyar.

A ranar ashirin da bakwai na watan Auguta, na’urar da hukumar ta tura cikin sararin samaniyar mai suna Juno ta dauki hoton, hoton na bayyanar da nisan tafiyar da na’urar tayi a cikin duniyar watan, da ya kai kimanin nisan kilomita dubu hudu da dari biyu 4,200.

A karon farko da wani mahaluki ya taba ganin hoton duniyar Jupita kenan, a tabakin shugaban binciken Mr. Scott Bolton, suna cigaba da kara samun bayanai, da suke bayyanar ma mutanen wannan duniyar yadda wasu duniyoyin suke.

Hakan zai kara bayyanar ma, mutane irin baiwar da Allah yayi a cikin duniyoyi, baya ga irin abubuwan da mutane kan iya gani a wannan nahiyar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG