Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Soji Su Yi Karin Haske Akan Dalilan Neman Mutane Uku Ruwa A Jallo


Rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilan da suka sa sunayen mutanen nan uku wato A’isha Wakil, wadda aka fi sani da suna Mama Boko haram, da dan jarida mai suna Ahmed Salkida, da kuma Ahmed Bolari a cikin wadanda take nema ruwa a jallo.

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa darakatan yada labarai na rundunar sojin Najeriya Burgediya janar Rabe Abubakar ya bayyana haka a wata lakca mai taken Media-military relationship Against Insurgency a babban birnin Abuja.

Yayin da yake bayani akan yadda rundunar sojin ta saka sunayen mutanen uku a cikin wadanda take nem, ya kara da cewa ba wai haka kawai aka saka sunayensu cikin wadanda ake nema ruwa a jallo bane, dalilin shine an gayyace su domin bada Karin haske akan abubuwan da suka sani da jami’an basu sani ba, ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya kada su nuna ra’ayin san rai akan mutanen da ake nema ruwa a jallo.

A cewar Abubakar, shekaru bakwai Kenan da sojoji suke yaki da ‘yan ta’adda kuma abubuwa da dama sun faru, ya kara da cewa suna kokarin ganin cewa dukan abubuwan da zasu aiwatar su kasance sun zo dai dai da bukatun kasa ba domin kansu ba.

Daga karshe ya bayyana cewa basu neman jama’a ruwa a jallo haka nan siddan dole akwai dalilan da suka sa haka kuma ba sun neme su domin su tsare su bane, suna neman su ne domin Karin haske akan wasu batutuwa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG