Yau litini 11 ga watan Yuli, rana ce da majalisar dinkin duniya ta kebe domin mayar da hankali akan bukatun al'umma, kuma maudu’in wannan rana ta wannan shekara shine tunawa da ‘ya’ya mata domin inganta makomarsu.
A wata hira da sashen Hausa na muryar Amurka yayi da Dr Aminu Gamawa akan muhimmancin wannan rana da kuma amfanin tunawa da ‘ya’ya mata domin inganta makomarsu, malamin yayi Karin bayani kamar haka.
“Wannan rana ce mai matukar muhimmanci domin idan aka yi maganar mace, zaka cewa kodai uwa ce kokuma ‘ya ko kanwa, kuma idan ka duba yawan mutanen dake a wannan duniya a yau, sun kai kusan sama da mutane miliyan dubu bakwai wato Biliyan bakwai kenan, a cikinsu kusan Biliyan biyu, wato miliyan dubu biyu dukkan su ‘yan tsakanin shekaru goma zuwa ashirin da hudu ne.
Yawancin wadannan ‘yan mata matasa kimanin kashi tara cikin goma na kasashe masu tasowa ne, domin haka akwai kalubale da dama dake fuskantar mata, misali al’umomi da dama basu cika ba mata cikakken ‘yanci ba, wato anfi fifita ‘ya’ya maza akan mata, kama daga karatun su zuwa irin yadda ake kula da karatun nasu da sauran abubuwa makamantan haka.
Baya ga haka akwai matsaloli da dama da rayuwar mata ke ciki, ta dalilin haka ne aka kebe wannan rana domin yin nazari da la’akari akan irin kalubalen da suka addabi mata musamman matasa domin ganin hanyoyin da suka fi dacewa a inganta rayuwarsu.
Saurari cikakken bayanin a nan