Ba a tsammanin Koriya ta Arewa zata fara ganin sakamakon sabon takunkumin da Amurka ta kakaba mata kai tsaye, amma masu raji kare hakkin bil Adama sunce matakin da aka ‘dauka zai ci gaba da matsawa Koriyar da shugabanta lamba.
A yau Alhamis Koriya ta Kudu ta nuna goyon bayanta ga matakin Amurka na saka shugaban koriya a cikin jerin mutanen dake cin zarafin bil Adama, tare da wasu mutane 22 kan rawar da suka taka wajen keta hakkin bil Adama.
A wata sanarwa jadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, tace “wannan yunkurin ya aika da sako a baiyane, ba wai kawai ga shugabanni ba, har ma da shugabannin dake kula da gidajen Yari da
Gandirebobi da ‘yan sanda da ma sauran jami’an tsaro, cewar duniya na ganin duk abinda suke an cin zarafin bil Adama, kuma ba za a kyalesu ba.”
Cikin shekara ta 2014, kwamitin MDD ya fitar da rahotan dake tattare da bayanan cin zarafin bil Adama da Koriya ta Arewa take, ciki har da kisan ba gaira babu dalili da batar da mutane ba tare da ansan inda suke ba, da kame mutane ba tare da aikata laifi ba, da gallazawa.