Wasu daliban jamiaar birnin Nairobi dake kasar Kenya sun kwashe shekaru biyu domin samar da wata na’ura da zata inganta rayuwar mata masu juna biyu da kuma lafiyar yara. Wadanda suka samar da wannan naurar wasu dalibai ne da ake kira Joel Kabete shi da takwaran sa, da suke aji guda a jamiaar.
Daliban sun kwashe shekaru biyu suna kirkirar wannan naurar wadda take agazawa jariri da nunfashi bayan haihuwarsa ko kuma lokacin da ake kokarin fidda shi daga mahaifa.
Sau tari kasar Kenya na sayo kayayyakin aiki na asibiti daga kasashen waje. Misali irin wannan na’urar ana sayar da ita a kasar waje akan kudin Amurka dala dubu 2, amma wannan da daliban suka kirkira za a iya sayar da ita akan kwatankwacin dala dari 5.
Joel daya daga cikin wadanda suka kirkiri wannan naurar wanda yake kwas din injiniya, yace sunyi anfani ne da kayayyakin cikin gida domin kyera wannan naurar. Dalibin ya kara da cewa wannan zai zame tamkar wata fadakarwa ce domin ko ana iya anfani da kayayyakin gida wajan kyera na’urar da zata anfani ba yara kawai ba harma da al’umma baki daya.
Ita dai wannan naurar mai fitar da kalar bulu daga cikinta zai rage yawan wani abu dake taruwa a hantar jariri wadda sau tari yake haifar da cutar shawara.