Tun kamun lokacin rani ya kankama a kasar Amurka, dubun dubatan mutane a yankin kudu maso yamma na kasar Amurka, na fuskantar matsanancin zafi. Wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu 4, zafin da akeyi a kasar Amurka, ya kai kimanin mizanin awon zafi 120F, wanda ake ganin hakan wani sabon abu ne a shekarar nan 2016.
A cewar rahoton hukumar “National Oceanic and Atmospheric” wannan shekarar tana daya daga cikin shekaru da su kafi zafi, idan aka hada ta da shekarun da suka gabata. Sun bayyanar da cewar zafi ya karu a fadin duniya, wanda hakan zai iya haifar da yawan cuttutuka a cikin jama’a.
Wannan rahoton na kara nuni da irin halin da mafi akasarin kasashe zasu shiga cikin ‘yan kwanaki kadan, na mawuyacin halin zafi. Don haka akwai bukatar mutane su kokarta gyara muhallan su, da tsafftace ire-iren abinci da sukeci, hakan akwai bukatar rage yawan mutane da suke kwana a cikin daki daya, haka da bude daki don samun iska mai inganci.
Akwai cuttutuka da suke yaduwa a cikin wannan lokacin na zafi, wanda sukanyi illa kamin a lura, don haka akwai tsananin bukatar mutane su yawaita yin wanka, tsaftar wajen zama, da yadda ake gudanar da rayuwar yau da kullun, don gujema fadawa cikin wani yanayi.