Kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai reshen jihar Sokoto mai shalkwata a jihar Kaduna tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da lamurran matasa ta shirya wata gagarumar ziyarar buda baki da matasa mabiya addinin kirista suka kaiwa al’umar Musulmai domin nuna kaunar juna da karfafa zaman lafiya dake wanzuwa a tsakanin al’umar musulmai da mabiya addinin kirista a jihar ta Sokoto.
Uban kasar Gagi Alhaji Ummar Jabbi shine ya shugabanci zaman na buda baki, kuma yayi bayanin cewa Allaha ya riga ya hada su zama da juna fiye da shekaru dari, kuma tun tarihi basu taba samun fituna tsakanin juna ba, kuma a cewar sa yadda duniya take tafiya yanzu, ana samun matasa da dama da basu da ilimin addini dan haka suka ga yazama wajibi su gaiyaci shugaban addinan biyu domin wayar wa da matasan kawuna.
Malamin ya kara da cewa ta hanyar zaunawa tare da shugabannin addinan biyu, a sha ruwa tare a kuma ci abinci tare zai nunawa matasan cewa addinin musulunci addini ne wanda ke fadakar da zaman lafiya, haka kuma addinin kiritanci shima yana fadakar da zaman lafiya, dan haka jawo matasa da nuna masu alfanun zaman lafiya ya wajaba.
A daya bangaren kuma, Rev Ahmadu Mamman wanda ya jagoranci tawagar kiristocin ya ce sun ji dadi kwarai ganin yadda iyaye kuma magabata musulmai suka gayyacesu domin shan ruwa a lokacin buda baki, ya kara da cewa wannan zumuncine da ya kamata a karfafa shi domin hakan ya zamewa matasa abin koyi tunda sune kashin bayan kowacce al’umma. Daga karshe ya bayyana irin farin cikinsa na zama daya al’umma day aba tare da nuna wani banbanci ba.
Zaman na buda baki ya sami halartar wasu hakimai daga yankin kasar Gagi, da jami’an ma’aikatar bunkasa lamurran matasa ta jihar Sokoto da malaman addinin musulunci da limaman kirista.
Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk sanyinna daga Sokoto a nan.