Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Goyon Bayan Kawo Karshen Matsalar Niger Delta


 Jakadan Amurka a Najeriya
Jakadan Amurka a Najeriya

A gefe daya kuma Amurka tace dole ne a kare hakkin dan Adam na dukkan ‘yan Najeriya a wannan matsalar..

Wata sanarwa data fito daga ofishin jakadancin Amurka dake Abuja tace ofishin na bin rahotannin dake nuna karuwar hare haren yan bindiga a yankin Niger Delta mai arzikin mai. ofishin ya nuna damuwarsa da irin wadannan hare hare sannan yace yana nuna goyon bayansa bisa kokarin kawo karshen wannan matsala cikin lumana ta hanyar tattaunawa.

Ofishin jakadancin na Amurka yace yayin da yake fatan za’a shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi, a gefe daya kuma yana nanata cewar dole ne a kare hakkin dan Adam na dukkan ‘yan Najeriya a wannan matsalar..

Jakadan ya bukaci ‘yan Najeriya dasu dage wajen cimma zaman lafiya na din din a shiyyar Niger Delta da kuma dasa harsashin kawo chanji ta hanyar samar da dama a fannin tattalin arziki da ayyukan raya kasa a wannan shiyyar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG