Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Najeriya Ya Lashe Kambun Sana'ar Gugar Gilashin Mota A Duniya!


Gugar Gilashin Mota
Gugar Gilashin Mota

A ganin wasu masana, sana’a madafar rayuwar yau da kullun, babu mahalukin da zai dukufa wajen neman na kanshi, kana ya wulakanta. Hakan kan tsaya ne akan wanda bashi da zuciyar nema, ko kuma yake rena sana’a. Babu wulakantatar sana’a a duniya saa wadda mutun ya rena.

A wani rahoto da gidan talabijin na CNN suka fitar, wanda ya nuna wani dan Najeriya, da ya lashe kambun mai sana’ar wankin gilashin mota na duniya. Abdulahi Olatoyan, an kore shi a jami’a shekaru da dama, tun bayan nan ya fuskanci matsananciyar rayuwa. Amma duk da haka bai karaya ba, ya shiga sana’ar goge gilashin motoci a bakin titi, inda ya kan samu kudin da yake yima kanshi lalura.

Duk a cikin wannan sana’ar da ya keyi, wanda ya dauke ta da matukar muhimanci, ya kan ji kamar za shi ofishin gwamnati ne a koda yau she ya shirya fita da safe. Yakan saka kaya irin na ma’aikatan banki kuma ya kare a bakin titi, don neman abun da zai taimaki kanshi.

Abdul, yace babban burin shi a wannan sana’ar shine, ya samu kudin da zai koma makaranta a nan gaba, don kuwa yana da yakinin cewar, ilimi shine garkuwar duk wani dan’adam. “Yace dalilin da yasa ya kama wannan sana’ar shine, baya da bukatar ya dinga yawo a kan titi baya yin wani abu. Domin kuwa bata gari zasu iya rudar shi wajen shiga wani aikin da bai dace da shiba.” An bayyanar da shi a matsayin mutun na farko a fadin duniya, da ya dauki sana’ar goge gilashin mottocin mutane don karbar abun goro da mutunci, wajen saka kaya masu kyau a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG