Hukumar kula da harkokin kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta ci hukumar kwallon kafa ta Najeriya tarar kudi dalar Amurka dubu biyar $5000 kwatankwacin Euro dubu hudu da dari hudu kennan a sakamakon abinda ta kira yawan jama’ar da ya wuce kimada rashin cikakken tsaro a lokacin da aka buga wasan nema shiga gasar cin kofin Afirka da aka yi tsakanin kungiyar Sper Eagles da kungiyar kwallon kafa pharaoh ta kasar Misira.
Hukumar ta yanke wannan hukuncinne a wani taron ladabtarwa da ta gudanar a Johannesburg babban birnin Afirka ta Kudu, inda tayi barazara sawa hukumarb kwallon kafar ta Najeriya takunkumi idan ta sake kwatanta irin wannan.
Idan za’a iya tunawa kusan sama da mutane dubu arba’in ne suka halarci filin wasan Ahmadu Bello dake jahar kaduna mai nauyin daukar jama’a dubu goma sha biyar kacal.
An yi ta ganin ‘yan kallo na hawan duk wani abunda zasu iya makalewa akai domin su kallin wasan.
Gwamnatin jahar kaduna ce ta budewa ‘yan kallon kofar samun kallon wasan ba tare da biyan wasu kudi ba, inda daga karshe kungiyar misiran ta lallasa ta Najeriya da ci daya da babu 1 – 0, wanda yasa Najeriyar shiga halin kaka nika yi wajan kai labari