Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Cuta Ta Barke A Cikin Jirigin Yawon Shakatawa!


A dai-dai lokacin da wani jirgin yawon shakatawa yake shawagi da mutane kusan dubu daya a cikin teku. Sai ga wata sabuwar cuta mai suna “Norovirus” ta kama kimanin mutane sama da dari biyu da hamsin da biyu 252, a cikin jerin mutane dari tara da sha tara 919, da suke cikin jirgin shakatawa na Balmoral. A cewar hukumar dakile cuttutuka ta kasar Amurka.

Sun samu damar dakile sama da kashi 27% na cutar daga yaduwa a tsakanin fasinjojin jirgin. Sun kuma bayyanar da alamun kamuwa da cutar, wanda za’aga mutun na fama da matsanancin ciwon kai, mura, amai da gudawa da ganin jiri na tsawon lokaci.

An dai kara daukar kwararan matakai wajen ganin an samar ma, sauran fasinjojin ingantacciyar lafiya, da kokarin ganin cutar bata yaddu zuwa ga sauran mutane ba. Hakan yasa wasu kwararrun likitoci sun shiga cikin jirgin don bada gudun mawar su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG