Kwana daya bayan da hukumar kayyade farashin Mai a Najeriya, ta bada sanawar maido da tallafin Mai babban Kamfanin Mai na kasa NNPC, yace batun ba haka yake ba.
Tsohon Ministan ma’aikatar Man Fetur, a Najeriya, Alhaji Umaru Dambo yace wannan batu na bukatar ayi bincike, yana mai cewa “kila Ministan Mai na yanzu bai gane kan abin ba baya haka kuma yanzu yakamata ayi bincike wadanda suka ce masa a janye aka ce an janye mai suka ce masa kuma yanzu aka dawo dashi”.
Janar manaja mai kula da hulda da jama’a na kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) Malam Garba Deen Muhammad, yace rashin fahimta aka samu tun farko yace tallafin Man fetur baya cikin kasafin kudi na bana saboda haka ba yadda za’ayi adawo dashi, abinda ya faru shine karamin Ministan Mai ya kawo wani tsari ne na yin amfani da yadda ake sayar da danyen Mai a daidaita yadda ake sayan fetur a Najeriya, idan kudin danyen Mai ya tashi farashin Mai zai tashi idan ya sauka haka farashin fetur zai sauka, toh wannan tsari shine bawai an dawo da tallafi bane.
Kwararre kan tattalin arziki a Najeriya, Dr Nazifi Abdullahi Darma na Jami’ar Abuja, yace wanna tsari na NNPC, yayi daidai.