A yayin da ‘yan Najeriya, ke jiran fara amfani da kasafin kudin shekara ta 2016, wani dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Neja, Bala Faruk Bida, yace a yanzu haka akwai wasu makudan kudade da aka raba masu domin su gudanar da aiyukan raya kasa a yakunan su.
Bala Faruk, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna babbar birnin jihar Neja, yana mai cewa ‘yan Najeriya, da dama basu da labarin wadannan kudade a saboda haka yace ya zama tilas jama’a sun sawa wakilansu idanu domin ganin an yi abinda ya dace da kudaden.
Yace yakamata su kamata gaskiya da adalci, ya kara da cewa “wannan kudin an ce ne akai su mazabu ne domin yiwa jama’a aiki ba kudaden sawa a aljihu bane, da yawan mutane basu jin motsin kudaden saboda haka muna sanarda ‘yan Najeriya, su tambayi ‘yan majalisar su ina nasu kason kuma mai za’ayi dashi.”
Hakazalika Bala Faruk, ya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawara akan kasafin kudin da ake jayayya akai, yana mai cewa ya karbi kasafin kudin ya rattaba hannu amma ya tabbatar an bi diddigi kasafin kudin an zartar dashi kamar yadda ya kamata, domin barnar da ‘yan majalisa keyi na hada baki da ma’aikata nan aiki yake.