Wata kafar labarai ta ce masu kungiyar kwallon kafar na ta Manchester City, ba zasu bai wa manajan kungiyar, Manuel Pellegrini, isasshen kudin sayen ‘yan wasan da yake so a watan Janairu ba.
Kafar ta ce ‘yan kasar Abu Dhabi da suka mallaki kungiyar, zasu fadawa Pellegrini a wata ganawar da zasu yi a mako mai zuwa cewa babu wadataccen kudin da zasu iya bayarwa don sayen ‘yan wasa a wannan lokacin a saboda ‘yan wasan da yake son saya, Marco Reus da Ross Barkley, ba zasu shiga kasuwa a lokacin saye da sayar da ‘yan wasa na watan Janairu ba.
City ta riga ta auna yiwuwar sayen wadannan ‘yan wasa biyu, kuma ta san lokacin da yawancin ‘yan wasan da take kwadayin saya zasu shiga kasuwa.
Pellegrini dai yana fatan City zata iya rike Frank Lampard, dan wasan da ta yi hayarsa daga kungiyar New York City FC ta nan Amurka, har zuwa tsakiyar watan Maris, watau kafin a shiga sabuwar kakar kwallon kafa a nan Amurka.
Haka kuma zakarun Firimiya Lig na Ingilar sun a auna yiwuwar saye dan wasan gaba na Southampton, Jay Rodriguez a watan Janairun, saidai sun sanya idanu sun a kallon yadda yake murmurewa daga ciwon da ya ji mahadar jijiyar kafarsa.