Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwayar Cutar Ebola Na Iya Zama Na Kwanaki 90 Cikin Maniyyin Namiji Ko Ya Warke


Kwayar Cutar Ebola (bayan da aka yi amfani da gilashin da ya kara girmanta yadda idon dan Adam zai iya gani)
Kwayar Cutar Ebola (bayan da aka yi amfani da gilashin da ya kara girmanta yadda idon dan Adam zai iya gani)

Idan har ka taba wani ruwan jiki na mai fama da cutar Ebola, to cikin gaggawa wanke wurin da ruwa da sabulu.

Kwayar cutar Ebola tana iya zama ne kawai a cikin jini, ko bayangida, ko amai, ko nonon uwa, ko gumi, ko maniyyin wadanda cutar ta nuna alamunta a jikinsu. Ba a iya daukarta ta iska ko kuma ta cizon sauro.

Tilas sai kwayar cutar ta shiga har cikin jikin mutum kafin ta iya kama shi. Kada ka taba idanunka, ko hanci, ko baki, kuma ka daure duk wani nwurin dake da gyambo a jikinka.

Idan kana kula da wani mai fama da cutar Ebola, ka tabbatar ka sanya safar roba ta hannu kafin ka taba zanin gado ko bargo ko mayafi ko kuma suturar maras lafiyar da watakila wani ruwan jikinsa ya taba su.

A guji yin jima’i da namijin da ya warke daga cutar Ebola. Kwayar cutar tana iya zama har na tsawon kwanaki 90 a cikin maniyyin namiji. Idan har ma ya zamo tilas a yi jima’i, to tilas a tabbatar anyi amfani da kororon roba.

Kwayar cutar Ebola ba ta iya rayuwa na lokaci mai tsawo a filin Allah. Hasken rana, da Bilich da kuma sifirit sun a kasha kwayar cutar.

Matakin farko na kare kai daga wannan cuta shi ne na wanke hannu a kai a kai da sabulu ko kuma maganin wanke hannu.

EBOLA - Yadda Ake Samunta Da Yadda Ba A Samunta - 1'43"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG