Wannan ita ce shekara ta biyu a jere da Aliko Dangote yake zamowa na daya a cikin ‘yan Afirka 40 da suka fi kudi. Mujallar Forbes ta ce Aliko Dangote yana da dukiyar da ta kai dala miliyan dubu 12.
Mujallar Forbes ta ce akasarin kudaden Dangote ya samu ne daga masana’antun yin simintinsa, wadanda suke a cikin kasashe 14 a Afirka.
A bayan Aliko Dangote, akwai wasu ‘yan Najeriya da dama cikin jerin mutanen da suka fi kudi a nahiyar Afirka, cikinsu har da Mike Adenuga wanda shi ne na 5, kuma yana da kimanin dala miliyan dubu 4 da 300; sai Jim Ovia wanda yake lamba ta 17, kuma yana da dukiyar dala miliyan 775; sai Theopilus Danjuma wanda ke lamba ta 21 da dukiyar dala miliyan 600.
Sauran ‘yan Najeriyar sun hada da Oba Otudeko wanda yake lamba ta 24 da dala miliyan 550; da Hakeem Bello Osagie wanda yake lamba ta 28 da dala miliyan 450; sai Abdulsamad Rabiu wanda yake lamba ta 29 da dala miliyan 400; sai kuma Mohammed Indimi dake lamba ta 30 da dala miliyan 330.