Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla 74 A Misra


A zub da jini mafi muni tun lokacin da sojoji suka tumbuke Mohammed Morsi daga kan mulki, an kashe 'yan zanga-zanga 74 a arangama da dakarun tsaron gwamnati

Hukumomin Misra sun ce an kashe mutane akalla 74 a arangama tsakanin dakarun tsaron gwamnati da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi daga jumma’a zuwa jiya asabar a biranen al-Qahira da al-Askandariyya.

Jiya asabar ta kasance daya daga cikin ranakun da aka fi zubar da jini tun lokacin da sojojin Misra suka hambarar da shugaba Morsi a farkon watan nan, suka kuma yi masa daurin talala.

Kungiyar Ikhwanul Muslimun (Muslim Brotherhood) ta Morsi ta ce haka siddan ‘yan sanda a al-Qahira suka bude wuta a kan ‘yan zanga-zangar da ba su dauke da makami a unguwar Nasr, inda ‘ya’yan kungiyar suka yi makonni su na zaman diris su na neman a maida Morsi a kan kujerarsa ta mulki.

Jami’an gwamnatin Misra sun musanta wannan, suka ce ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa ne kawai, kuma magoya bayan Morsi dake maci sune suka haddasa wannan tashin hankalin.

A al-Askandariyya, hukumomin Misra sun ce mutane daga cikin wani masallaci sun yi harbi kan gidajen dake kewaye da nan a jiya asabar, amma magoya bayan Morsi sun ce ‘yan bindiga ne suka je suka yi harbi kan mutanen dake cikin wannan masallaci.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya bayyana wannan lokaci a zaman mai matukar muhimmanci ga makomar Misra, yana mai gargadin cewa zub da jini ci baya ne ga kokarin sasanta al’umma da kafa dimokuradiyya.

Yace alhaki ne a kan hukumomin Misra su tabbatar da mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki da na yin taro. Yayi kiran da a gudanar da bincike na Allah da Annabi kan wannan zub da jini na baya-bayan nan.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG