Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sandy Zata Iya Yin Barna Mai Yawan Gaske A Amurka


Masana yanayi na Amurka su na bin sawun mahaukaciyar guguwa mai suna Sandy ta tauraron dan Adam, jumma'a 26 Oktoba 2012 a Miami
Masana yanayi na Amurka su na bin sawun mahaukaciyar guguwa mai suna Sandy ta tauraron dan Adam, jumma'a 26 Oktoba 2012 a Miami

Ana sa ran Sandy, wadda ta kashe mutane 43 a yankin Carribean, zata shafi miliyoyin mutane a tsawon yankin gabashin Amurka

Mahaukaciyar guguwa mai suna Sandy ta doso kan bangaren gabashin Amurka, inda masana suke kyautata zaton cewa zata ci karo da wata iska mai sanyi dake fitowa daga arewa, ta haddasa mummunan hadarin ruwan sama da guguwar da zasu iya yin barna mai yawan gaske.

Jami’ai suka ce wannan mahaukaciyar guguwa da hadarin ruwan saman tekun dake tattare da ita zasu gawurta su girma ta yadda zasu iya mamaye yankin gabashin Amurka, inda zasu juye ruwa da iska, da ambaliya da katse wutar lantarki da kuma juye dusar kankara.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya tattauna yadda za a takali wannan mahaukaciyar guguwa dake tafe yau asabar tare da jami’an gwamnatin tarayya, cikinsu har da sakatariyar ma’aikatar tsaron cikin gida, Janet Napolitano da kuma shugaban Hukumar Ayyukan Gaggawa ta Tarayya, Craig Fugate. Fadar White House ta ce shugaba Obama ya umurci hukumar kula da ayyukan gaggawar da ta tabbatar da cewa ta samar da dukkan kayayyakin da take iyawa don tallafawa masu ayyukan gaggawa na jihohi da kananan hukumomi.

Ranar talata da asuba ake sa ran idanun mahaukaciyar guguwar ta Sandy zai iso kan doron kasa daga teku a gabar gabashin Amurka.

Cibiyar Nazarin Mahaukaciyar Guguwa mai tattare da ruwan sama ta Amurka, ta ce Sandy ta rikide ta koma mai tattare da iskar dake da karfin mahaukaciyar guguwa wadda fadinta ya kai kilomita 160 a gefe guda kawai daga idanunta.

Ana sa ran Sandy zata shafi miliyoyin mutane a nan yankin gabashin Amurka, kama daga Jihar Florida a kudu har zuwa bakin iyaka da kasar Canada a arewa. Ruwan sama da iskar dake tattare da Sandy sun kashe mutane akalla 43 a lokacin da ta ratsa ta kan kasashen dake yankin tekun Carribean.

Tuni har jihohin New York, da Pennsylvania, da Maryland da Virginia da Carolina ta Arewa da kuma nan Washington Gundumar Columbia suka ayyana kafa dokar-ta-baci. Kamfanonin wutar lantarki sun ce jama’a su shirya ma dauke wuta, yayin da aka shawarci jama’a da su adana ruwa a robobi da abincin gwangwani da kuma batura.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG