Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Bullar Fari A Nijar Da Mali


Damina ta sauka sosai a arewacin Mali da Niger, cikin mako uku da suka wuce, sakamkon haka kuma sai aka sami pullar fari.

Damina ta sauka sosai a arewacin Mali da Niger, cikin mako uku da suka wuce, sakamkon haka kuma sai aka sami pullar fari. Yanzu an fara daukar matakai na shawo kan kwarin a yankin da tuni yake fama da matsalar karancin abinci. Ga rahoton da wakilin Muryar Amurka Joe De Capua, ya hada mana.

Ana iya kiran su farin hamada, amma suna son ruwan sama. Keith Cressman shine babban jami’in majalisar dinkin duniya a hukumar abinci da aikin noma, wanda aikin sa ne hasashen pullar fari da kwari:

Dama fari suna pulla, da kuma zama a galibin lokuta a yankin Hamada tsakanin kasashen dake Afirka ta yamma, da kuma arewacin India. Abinda suke bukata shine ruwan sama domin su hayayyafa. Ruwan sama yana samar da danshi ga kasa domin kwayayensu, wadanda suke kenkeshewa bayan kamar mako biyu. San nan bayan kamar mako shida, ‘ya’yan farin da basu da fukafuki sai su girma.

San nan idan ruwan sama yayi yawa ainun kamar yadda aka samu yanzu a arewacin Mali da Nijar, to wuri ya samu domin bullar kusan abinda za’a kira garke:

Sun san samu wuri. Kuma idan suka yi haka, nan da nan zaka ga sun hayayyafa sun yadu da yawan gaske. To a wan nan lokacin ne fa zasu iya barazana sosai ga gonaki a kasar.

Cikin watan jiya ne aka bada labarin farin sun iso Mali da Nijar, daga Aljeriya da Libya, inda aka bada labarin bullarsu cikin watan Janairu. Hukumar abinci ta duniya tace rashin tsaro a Aljeriya da Libya sun hana daukan matakai, hakan ya baiwa farin damar kaura ta ratsawa a fadin Hamada.

Cressman yace ruwan sama kamar da bakin kwariyar, ya samar da yanayi mai kyau domin su hayayyafa, amma hakan yana iya samar da wani sabon rukuni na fari a wata daya ko biyu, masu zuwa. Wadan nan sabbin jinin zasu sake zama sabuwar barazana ga Aljeriya da Libya, san nan suyi barazana ga kasashe dake yammacin Afirka dake yankin Sahel.

Idan zaka iya kwatanta garken fari, daga nesa idan ka gansu zaka zaci hadari ne, a garken akwai fari milyan dubu daya, to karamin bangare na garken zasu iya cinye abincin da mutane dubu biyu d a dari biyar zasu ci a rana daya.Sabo da haka idan aka sami garke-garken fari a cikin wata kasa, zasu iya illa sosai ba akan gona ki kadai ba, amma har da janyo matsalar karancin abinci sosai.

Kodashike an fara daukar matakan yin feshi a Nijar tun a farkon watan Yuni, rikicin da ake yi a arewacin Mali ya hana a dauki irin wadan nan matakai. An sace motocin a kori-kura, da wasu kayan aikin maganin farin da wasu kwari, a kasar.

Hukumar abinci ta duniya tana neman dala milyan $10 domin ta fadada aikin dakile fari da wasu kwari. Wan nan kari ne kan abinda ake kashewa cikin kasa. Cressman yace idan aka kashe dala milyan $10 hakan zai sa a’ adana dala milyan dari biyar a shekara ko fiyeda haka, wadan da za a kashe wajen kokarin shawo kansu idan ba a yi tun farko ba.

Haka kuma hukumar tana sa ido sosai kan bullar fari a gabashin cadi da yankin Darfur a Sudan.

XS
SM
MD
LG