Mr. Obama yayi kira ga magoya baya yau laraba a Jihar Iowa, da su jefa masa kuri'unsu domin ya kammala aikin ci gaban da ya ce ya fara samu a kan batutuwan tattalin arziki.
A lokacin da yake magana game da muhawarar ta jiya, shugaban yace a zahiri, ajandar Romney mai matakai biyar, mataki guda kawai ta kusa na nuna gatanci ga attajirai.
Shi kuma Mr. Romney, ya fadawa magoya baya a Jihar Virginia cewa Mr. Obama ba ya da wata ajanda ta wa'adi na biyu kan karagar mulki. A ci gaba da kokarinsa na mayar da hankali a kan tattalin arziki, Romney yace shugaban ba ya da wani shirin kirkiro sabbin ayyukan yi kuma Amurkawa marasa karfi zasu fuskanci karin haraji har na dala dubu 4 a shekara idan aka sake zaben Mr. Obama.
Nan gaba a yau laraba, Mr. Obama zai tafi Jihar Ohio, yayin da Mr. Romney zai sake yada zango a wani yankin na Jihar Virginia.
Shugaba Obama yana fata cewar zai kara samun zabura daga irin rawar ganin da yayi a muhawarar jiya talata. Kuri'un neman ra'ayoyin masu jefa kuri'a da aka yi dab da kammala zaben sun nuna cewa Mr. Obama ya doke tsohon gwamnan na Jihar Massachussetts a muhawarar ta jiya, abinda ya sha bambam da muhawarar farko.