A cikin muhawarar da aka gudanar a wata karamar makarantar jami’a dake jihar Kentucky da aka yayata a tashoshin talabijin na kasar, Biden ya dorawa jam’iyar Republican alhakin tabarbarcewar tattalin arzikin kasar.
Ryan ya maida martani da cewa, shugaba Obama da ‘yan jam’iyar Democrat a majalisa sun shiga ofis a shekara ta dubu biyu da takwas inda jam’iyar take da rinjaye, wannan kuma ya basu damar yin dukan abinda suke so. Yace gwamnatin ta shaidawa Amurkawa cewa, idan aka amince da tsarin zaburar da tattalin arziki zai habaka tattalin arzikin kasar da kashi 4% amma tattalin arzikin ya cira ne da kashi 1.3% bisa dari kawai.
Da yake magana a kan harkokin kasashen ketare Biden ya bayyana harin da aka kai kan ofishin jakadancin Amurka a Libya a matsayin abin takaici, tare da alkawarin cewa, ko da wanne kuskure ne aka yi, ba za a sake maimaitawa ba.
Ryan ya kushewa gwamnatin shugaba Obama domin gaza samar da cikakken tsaro a Benghazi da kuma daukar makonni biyu kafin su amince da cewa, harin ta’addanci ne.
Yace “Jakadenmu a birnin Faris yana da mayakan ruwa dake gadinsa, Bai kamata mu sami rundunar mayakan ruwa da zata yi gadin jakadenmu a Benghazi ba, inda muka sani cewa, akwai kungiyar al-qaida dake da makamai?”
Mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa, ba a shaidawa shugaba Barack Obama cewa ana bukatar karin jami’an tsaro ba.
Game da Iran kuma. Ryan yace jamhuriyar Islaman ta yi karfi sabili da ba a yarda da gwamnatin Obama dangane da ayyukan nukiliya na Iran. Biden ya musanta haka da cewa, Amurka ta kakabawa kasar takunkumi mafi tsauri da aka taba kakabawa Iran a tarihi.