Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Gwabza Fada Da Mayaka A Jihar Yobe


Wani jami'in tsaro kenan a wani wurin da 'yan Boko Haram su ka kai hari
Wani jami'in tsaro kenan a wani wurin da 'yan Boko Haram su ka kai hari
Rundunar sojin Nigeria ta bada rahoton gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan da ake kyautata zaton ‘yan Boko haram ne jiya lahadi a jihar Yobe.

Sojojin suka ce sun hallaka mayakan da ake zaton ‘yan Boko haram ne guda Talatin.

Babban jami’in dake Magana da yawun rundunar sojin Nigeria ya bada labarin cewar, daga cikin wadanda sojojin Nigeria suka kashe harda wani baban jami’in kungiyar Boko Haram.

Yace sojojin Nigeria sun kuma sami nasarar kwace makamai masu yawa. Yayinda aka kuma kame mayakan Boko haram goma ana tsare dasu, suna kuma bada hadin kai wajen yiwa jami’an tsaron Nigeria bayani kan hanyar da za’a bi domin kamo sauran
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG