Rediyo
Yau da Gobe 1530 UTC (30:00)
Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da kayatarwa, ya kuma karfafa mu su samun kaifin fahimtar matsalolin da suka addabe su, suka dabaibaiye su a wannan zamani. Shirin Yau da Gobe na zuwa sau biyar a mako, Litinin zuwa Jumma’a, daga karfe 4 da rabi na yamma zuwa karfe 5! Yau da Gobe ya hada komai, daga filin dafe-dafen gargajiya, zuwa zauren matasa inda suke bayyana ra’ayoyin su daban-daban akan wasanni, da siyasa, da mu’amala ta samari da ‘yan mata, da fasaha, da filin kiwon lafiyar matasa.
Shirin Dare 2030 UTC (30:00)
A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.