Wani matashi a jihar Kaduna ya kirkiro karamin jirgi mara matuki da zai iya gano cututtukan shuka a gonaki; Hukumomi a Kamaru su na gargadin iyaye da su guji karya dokokin hana sa yara aikin karfi; wata kungiya na tara abinci don taimakawa mabukata a Lagos, da wasu rahotanni
Adadin wadanda suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen a yammacin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya karu zuwa akalla 29 tare da gano akalla mutum 128 da suka tsira da rayukansu, wasu kuma ba a san adadinsu ba, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a ranar Alhamis.
Ukraine ta kai wani babban hari a birnin Moscow a ranar Laraba tare da harbo jiragen sama mara matuka guda 11 da jami'an tsaron kasar Rasha suka ce na daya daga cikin hare-hare mafi girma na jirage marasa matuka akan babban birnin kasar tun bayan yakin na Ukraine da aka fara a watan Fabrairun 2022.
Domin Kari