Mazauna Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijar sun bayyana ra’ayoyinsu game da fahimtar irin fasahohin da mutane ke amfani da su wajen inganta rayuwasu.
Wata Kungiyar agaji mai ofisoshi a kasashen Kenya da Amurka mai suna InAble, ta na da burin kawo sauyi ta yadda za ta tallafawa matasan Afirka masu fama da tawaya wajen sama musu kayan fasaha na taimakawa rayuwa.
An kiyasta cewa mutane biliyan 2.5 ne suke bukatar akalla wata na’ura mai saukaka rayuwarsu sannan galibi mutane suna bukatar fasahohin zamani masu saukaka rayuwa a wani lokaci a rayuwar su.
Wasu mazauna Kaduna a Najeriya sun bayyana matakin da su ke dauka don ganin suna shaker iska mai kyau
Wata kwararriya a Maiduguri, Dr Aida Abba Wajes ta yi karin haske akan illolin gurbatacciyar iska ga lafiyar mutane da kuma matakan da za a iya dauka.
A kasar Kenya, daliban wata makaranta dake kusa da inda ake zubar da shara mafi girma a kasar sun fara dashen itatuwan gora don bunkasa ingancin iska a yankin.
Ingancin iskar da muke shaka kullum yana da tasiri ga lafiyar mu. Sinadarin Sulfor dioxide da sinadarin carbon monoxide suna daga cikin sinadaren da suke gurbata iskar da muke shakka a fadin duniya.
Domin Kari