Ukraine: Wani dan jaridan Rasha, Arkady Babchenkp ya fito a bainar jama’a kwana daya bayan da aka ce an kasheshi. Babchenko ya ce ya yi hakan ne domin taimakawa hukumar leken asirin Ukraine wajen kama masu kokarin kasheshi,.
Mali: Sakatare janar na MDD, Antonio Guterres ya isa garin Sevare da ke tsakiyar Mali, a rana ta biyu ta ziyarar da ya ke yi a kasar da majalisar ke aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya.
Rundunar sojojin Nijeria ta sha alwashin cigaba da farautar yan boko haram a duk inda suke, Birrgediya janar Ibrahim Manu Yusuf,kwamanda mai barin gado tare da Birgediya janar Abdulmalik Bui wanda zai maye gurbinsa a Maiduguri jihar Borno.
DRC: Ma’aikatan lafiya na ci gaba da gwada allurar rigakafi da wayar da kawunan jama’a a kan cutar Ebola, data hallaka akalla mutane 22 da kuma kama sama da mutane 30 a kasar.
Palasdinawa 13 suka sami raunika bayan dakarun Isra’ila sun kai hari kan sannsanin ‘yan gudun hijira yayin da suke neman wadanda ake zargi da hallaka sojan Isra’ila.
Russia: Shugaba Vladmir Putin ya karbi bakuncin takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, dukkan su kuma sun nuna takaicin su kan Shugaba Donald Trump da ya soke taron kolin da aka shirya zai yi da Koriya ta Arewa.
Junhuriyar Afrika ta Tsakiya: Mutane goma sha biyu aka kashe a gundumar Bangui mai rinjayen musulmai bayan wani gurneti ya tashi a yayin da ake kwafsawa tsakanin mayakan Musulmi na Seleka da kungiyoyi masu adawa da Balakas da kuma wasu bangarori na al’umma
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da soke taron kolin da aka shirya yi ranar 12 ga watan Yuni, a wata wasika da ya aikawa shugaban Koreya Ta Arewa Kim Jong Un.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce sojojin Najeriya sun aikata laifukan keta hakkin bil’adama a lokacin da suke yaki da ‘yan Boko haram
Pakistan: An yi jana’izar wata daliba daga Pakistan da ke karatu a Amurka karkashin shirin musayar dalibai wadda aka bindige makon da ya gabata a harin a makarantar da take.
Nigeria: An yi jana’izar wasu pastoci biyu da masu ibada 17 bayan wata daya da kai masu hari a coci, na baya bayan nan a jerin tashe-tashen hankula da ake asarar rayuka mai nasaba da addini.
Cameroon: An gudanar da bukin hadin kan kasa na 46th a Buea dake kasar Kamaruduk da cewa ‘yan awaren kasar sun bukaci jama’a kada su halarci taron
Venezuela: an sake zaben Nicolas Moduro na wa’adin shekaru shidda a zabe mai cike da takaddama da ‘yan adawa da shugabanni suka kira mara sahihanci
Domin Kari