Kamaru: Gwamnati ta ce za ta rufe kan iyakokinta tare da dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen fasinjoji na dindindin, bayan sanarwar da samun mutum na biyar da ya kamu da cuta.
Kasar Sin: Gwamnatin kasar ta kwace izinin aikin wasu 'yan jaridun Amurka na jaridun Amurka uku, lamarin da ya kara munana fadan da ke tsakanin manyan kasashen biyu na duniya da ya shafi barkewar cutar coranavirus da' yancin kafofin watsa labarai.
A Italiya an samu karin mutuwar mutane 349 daga cutar Coronavirus, da kuma karin adadin wadanda suka kamu sama da 27,000.
Kasar Ivory Coast, ta rufe iyakokin ta ga wasu 'yan kasashen waje da ke da yawan adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus, ta kuma rufe makarantu da jami'o'i na tsawon kwanaki 30.
A Nijar Kilishi dai wani abinci ne wanda ba ma a Niger da Najeriya kadai ya yi suna ba har ma da sauran kasashen duniya. Wani mai yin kilishi a Nijer ya bude wata masana’anta ta sarrafa kilishin a zamanace duba da cewa tsaftar muhalli na da muhimmanci a wannan sana’ar.
Najeriya: Wani bututun gas ya fashe a wani kamfanin sarrafa iskar gas a Legas jiya Lahadi, inda ya kashe a kalla mutane 17. Wasu mutane da dama sun ji rauni, sannan gine-gine sama da 50 sun rushe sakamakon fashewar.
Spain: , yayin da ta kasance kasa ta baya-bayan nan da ta rurrufe dukkan hada-hada da nufin rage yaduwar cutar.
Hukumomin gwamnati sun tabbatar da bullar Coronavirus na farko a kasar, sun ce mutumin dan kasar ne wanda ya dawo da ga Iyaliya. Sun kuma kara da cewar yana Asibiti cikin koshin lafiya, kana an killace shi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya saka dokar hanawa Turawan yammaci shiga kasar na takaitaccen lokaci, a lokacin da ya ke magana da ga ofishinsa na Oval, wanda ba'a saba ganiba. Amma ya ce hurdodin kasuwanci za su cigaba da gudana a tsakanin su da kasashen.
Afghanistan: Karar fashe-fashen rokoki ya tarwatsa bukukuwan rantsar da shugaban kasa biyu a lokaci daya, Ashraf Ghani da Abdullah Abdullah yau Litinin a Kabul. Kowanne daga cikin su biyun masu adawa da juna ya ƙi amincewa da rantsar da dayan.
A kasar Togo an sake zaben Shugaba Faure Gnasssingbe a wa’adin mulki na hudu, nasarar da ta tsawaita shekara 15 da ya kwashe yana mulki. A zagayen farko, Gnassingbe, ya samu kashi 72 na kuri’un da aka kada.
Domin Kari