Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da tawagar shi sun isa birnin Santambul na kasar Turkiyya domin halartar taron bunkasa cinikkayya tsakanin kasashen Afirka da Turkiyya wanda za a yi karo na uku.
Malam Garba Shehu jami’in ya’da labarai a fadar Gwamnati wanda ke cikin tawagar Shugaban kasar ya kwatanta wannan ziyara a matsayin mai muhimmanci.
“Muhimmancin wannan taro shi ne don a hada kai tsakaninmu da su, don a ci moriyar irin ci gaba da Turkiyya take samu, mu samu karuwa da su ta wajen zuba jari da su ke yi a kasashe daban daban.” In ji Garba Shehu.
Ya kara da cewa ci gaba da arziki da Turkiyya ta samu musamman a wannan zamani tana bazata a duniya kuma kasashen Afirka ma suna so su amfana da wadannan abubuwa.
“Mu a matsayinmu na Najeriya, tanadi ne da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a wannan taro shi ne, in banda wannan taro tsakanin kasashen Afirka da Turkiyya mun zo da Jami’an gwamnati na sassa daban daban wadanda ake so a yi taruka a gefen fage tsakanin kasa da kasa, taron nan ko In sha Allahu za’a fara tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Recep Erdogan su biyu za su fara tattaunawa.
“Turkiyya tana da niyya kuma sun nemi a nuna musu inda za su kafa muhimman abubuwa a Najeriya kamar irin otal otal, manyan dakin taruka na zamani, asibitoci, makarantu da irin wadannan abubuwa.” Shehu ya ce.
Akwai dai yarjejeniya daban-daban da aka sanyawa hannu a lokacin da Recep Erdogan ya zo ziyara Abuja a kwanan baya inda aka bayar da wannan goron gayyata, a ciki har da maganar tsaro da kayan yaki da za’a taimakawa na Najeriya a cewar kakakin Buhari.
Kasar Turkiyya dai ta samu ci gaba cikin karamin lokaci wajen kere-kere na kayyakin yaki, musamman wadannan sababbin jirage wadanda ba su da matuki (drones.)
A lokacin ziyarar da ya kai Najeriya, Recep Erdogan ya fada cewa wannan yaki da suke yi da ta’adanci da masu satar mutane, da masu satar dabbobi, Boko Haram, a shirye suke su yi aiki da Najeriya.
A cikin tawagar Shugaba Muhammadu Buhari akwai Ministan Tsaro, akwai mai ba shi shawara akan harkar tsaro, akwai shugaban shashen aikin leken asirin Najeriya.
Saurari cikakkiyar hirar Umar Faruk Musa da Malam Garba Shehu:
Your browser doesn’t support HTML5