Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, ya kai ziyarar yini daya kasar Nijer, a ci gaba da rangadin da yake yi na wasu kasashen nahiyar Afirka.
Wannan shine karo na farko da shugaban Faransa Francois Hollande ya ziyarci kasar ta Nijer, inda aka yi masa kyakkawan tarbo.
Shugaban ya gana da shugaban kasar Nijer, Issoufou Mahamadou, a fadar gwamnatin kasar ta Nijer.
Wasu ‘yan kasar ta Nijer da suka zo domin yiwa bakon maraba sun ce sun yi murna da ziyarar, domin a cewar su idan ba’a samun bako a kasa aikin banza ne kuma in ba’a yaba da kasar ka ba, ba’a zuwa .
Shugaba Hollande, ya ziyarci daya daga cikin sansanonin sojoji Faransa dake kasar Nijer, inda Faransa ta girke jiragen yaki da makamai domin tabbatar da tsaro a kasashen yankin sahel.
Your browser doesn’t support HTML5