Zinedine Zidane Ya Ki Amincewa Da Aikin Horar Da Kungiyar Real Madrid

Tsohon shugaban kulob din Real Madrid Ramon Calderon ya shaida wa mane ma labarai cewar, tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ki amince wa da yin aikin horar da kungiyar Real Madrid a karo na biyu.

Zidane mai shekara 46 da haihuwa, ya ajiye aiki a kungiyar ne a karshen kakar wasan bara, kwana biyar bayan da ya jagorance ta lashe kofin zakarun Turai karo na uku a jere.

Calderon ya ce "shugaban kungiyar Real Madrid Florentino Perez ya kira Zidane ta waya yana neman sa da ya dawo kungiyar, amma Zidane ya ce ba yanzu ba, akwai yiwuwar ya karbi aikin a watan Yuni.

Bayan haka tsohon shugaban Roman Calderon, ya ce akwai yiwuwar dawowar tsohon kocin Manchester United da Chelsea Jose Mourinho wanda kuma ya horar da Madrid daga shekarar 2010 zuwa 2013.

Shugaban kungiyar ya fi bukatar Jose Mourinho. Amma tsohon shugaban Real Madrid, Roman Calderon ya ce dawo da Mourinho kuskure ne babba" .

Ana sa ran Real Madrid za ta yi gagarumin garambawul a kakar wasa mai zuwa bayan kashin da ta sha a hannun Ajax wadda ta kore ta daga gasar Zakarun Turai, da kuma wasu kofuna da ta rasa ciki harda El Clasico inda Barcelona ta yi waje da ita a zagaye na daf da karshe.