Zinaden Zidane: Angulu Ta Koma Gidanta Na Tsamiya

Zinedine Zidane na kungiyar Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sake dawo da tsohon kocinta Zinaden Zidane, a matsayin mai horas da tawagar ta, bayan ya barta kusan watanni 10 a son ransa.

Zidane ya jagoranci kungiyar ta Real Madrid har ta lashe kofin gasar zakarun Turai sau 3 a jere a lokacin da yake aiki. Zidane ya maye gurbin kocin Real Madrid Santiago Solari, bayan da ya gaza tabuka abun kirki a kungiyar.

Real Madrid ta sake kulla yarjejeniyar shekaru uku da Zidane, wanda za ta kare a ranar 30 ga watan Yuni, na shekarar 2022.

Zidane ya komawa Real Madrid a dai-dai lokacin da ya rage wasanni 11 kawai a kammala gasar La Liga ta bana, wanda kungiyar ke mataki na uku da maki 51, tazarar maki 12 tsakaninta da babbar abokiyar hamayya Barcelona da ke jagorantar La Ligar da maki 63.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, Zidane ya ce ya yanke shawarar dawowa kocin Real Madrid ne, saboda kaunar kungiyar da yake da kishinta, dan haka a lokacin da shugabanta Florentino Perez ya tuntube shi, sai ya kasa kin amsa bukatarsa.

Tun a lokacin da Barcelona ta lallasa Real Madrid a jere a gasar la Liga da ta Copa del Rey aka sa ran za a kori kocin Madrid a wannan lokaci wato Santiago Solari, amma sai aka jinkirta, daga bisani kuma Ajax ta fitar da
ita daga gasar zakarun Turai, hakan ya sa Real Madrid ta yi barin Kofuna uku
cikin mako guda.

Zidane zai fara jagorantar kungiyar a wasan da zata buga tsakanita da Celta Vigo, Santiago ranar Asabar 16 ga watan Maris cikin gasar Laliga mako na 28 karo na biyu a karawar farko Madrid ta doke Celta Vigo daci 4-2 a gidanta.