Zelensky Ya Yi Allawadai Da Harin Rasha Kan Turakun Lantarki A Ranar Kirsimeti

Wannan shine mummunan hari na 13 kan turakun lantarkin Ukraine, kuma shi ne samamen Rasha na baya-bayan nan kan tsarin lantarkin kasar a wannan hunturun.

A yau Laraba Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi allawadai da harin rashin tausayin da Rasha ta kai, inda ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka 170 kan turakun lantarkin kasar da yaki ya daidaita a ranar Kirsimeti, tare da hallaka ma'aikacin lantarkin guda.

Kasar ta wayi gari da jin karar na'urar dake ankarar da kawo hari ta sama da misalin karfe 5 da rabi na asubahin yau, sannan rundunar sojin saman kasar ta ba da rahotanin cewa Rasha ta kaddamar da harin makami mai linzami samfurin Kalibr daga bahar aswad.

Wannan shi ne mummunan hari na 13 kan turakun lantarkin Ukraine, kuma shi ne samamen Rasha na baya-bayan nan kan tsarin lantarkin kasar a wannan hunturun.

A wani labarin kuma, Rasha ta ce hare-haren Ukraine da fadowar wani jirgi maras matuki sun hallaka mutane 5 a yankin Kursk da ke kan iyaka da arewacin Ossetia dake yankin Caucasus.

Ukraine ta bayyana cewa rundunar sojin samanta ta kakkabo 58 daga cikin makamai masu linzami 79 da Rasha ta harba mata.

Sai dai ba ta iya kakkabo makamai masu linzami guda 2 kirar Koriya ta Arewa samfurin KN-23 da Rasha ta harba ma ta ba.

Mahukuntan birnin Kyiv sun kara da cewa wani makami mai linzamin da Rasha ta harba ya keta sararin samaniyar kasashen Moldova da Romania, sai dai Romania ta ce ba ta iya gano hakan ba a yayin da Moldova ta ce tana bincike.